12 Nuwamba 2019 - 05:14
Ministan Man Fetur Na Iran Ya Bayyana Cewa; Kasar Ta Samu Karin Man Fetur Da Ya Kai Ganga Biliyan 22

Ministan man fetur na Iran wanda yake tsokaci akan gano wasu sabbin yankuna na man fetur ya ce; Sabon wurin da aka gano yana da gangar man fetur biliyan 53 a kudancin Khuzistan, kuma dama a can baya an gano wani wurin mai dauke da ganga biliyan 31, ga shi kuma yanzu an gano wasu gangunan biliyan 22

(ABNA24.com) Ministan man fetur na Iran wanda yake tsokaci akan gano wasu sabbin yankuna na man fetur ya ce; Sabon wurin da aka gano yana da gangar man fetur biliyan 53 a kudancin Khuzistan, kuma dama a can baya an gano wani wurin mai dauke da ganga biliyan 31, ga shi kuma yanzu an gano wasu gangunan biliyan 22

Beijin Zaginah ya ci gaba da cewa; wurin da aka gano yana daga cikin wuraren da suke fi zama masu dauke da man fetur a fadin Iran.

Ministan man fetur din na Iran ya kara da cewa; A baya an sami wasu yankunan masu dankare da man fetur a yankuna Mansuri, Sabuhri, Jafiri da Ab Taimur da Susgandar.

Zanginah ya kara da cewa; Tun a 2016 ne aka fara ayyukan gano man fetur a cikin wannan yankin, kuma tuni an haka rijiyoyi uku da suke kunshe da ganga biliyan 31.

Kimar sabbin ganunan man fetur din da aka gano sun kai dalar Amurka biliyan 32




/129